Take a fresh look at your lifestyle.

KANFANONI MASU LASISI KADAI ZASU SAYI KAYAN GONA DAGA HANNUN MANOMAN NAJERIYA – GWAMNATIN TARAYYA

83

Gwamnatin tarayya tace kanfanonin da ta baiwa lasisi a Najeriya kadai zasu iya sayen kayyakin masarufi kai tsaye daga hannun manoman Najeriya domin sayar wa alummar kasashen waje.

An samu amincewar hakan ne daga taron majalisar zartarwa ta tarayya ranar Laraba.

Hakan zai bai wa Manoman Najeriya kariya daga alummomin kasashen waje da mataimakan su dake sayen anfanin gona daga hannunn manoman kasa ba tare da kayyadadden farashi ba.

Ministan ciniki, Masanaantu da saka jari, Niyi Adebayo, shine ya sanar wa manema labaran fadar shugaban kasa jim kadan bayan taron,yace ya mika bukatu ga majalisar domin bunkasar harkokin gona a Najeriya.

“Wannan bukatar ta zama wajibi saboda ya kamata gwamnatin tarayya ta kafa hanyoyin da suka dace wajen kare martabar manoman Najeriya da samar da kyakyawan farashin da ya dace na anfanin gonar da suka noma domin bunkasa harkokin noman su.

“Sama da shekaru yan kasashen waje sun shioga sako sako a kasar suna sayen anfanin gona kai tsaye daga hannun Manoma a farashin da yayi musu dadi,kuma hakan zai rinka kawo cikas ga manoma.

“Saboda haka,daga karshe mun samu amincewar majalisar dattawan kasa FECgame da lasisi ga kananan kanfanoni da sukayi rajista da hukumar da ta dace na sayen kayayyakin masarufi kai tsaye daga hannun manoma.kuma wannan tsarin zai hana yiwa manoma wayon sayen kayayyakin gona da arha daga hannun su .”

LADAN NASIDI

Comments are closed.