Take a fresh look at your lifestyle.

NAJERIYA DA KUBA ZASU BUNKASA HARKOKIN AL’ADUN SU

Ladan Nasidi

0 156

Gwamnatin Najeriya da Kuba sun shirya bunkasa dangantakar al’adu tsakanin juna.

Babban Daraktanl, Cibiyar Al’adu da zaiyana ta tarayya, NCAC, Mr. Olusegun Runsewe ya sanar da haka lokacin da Jakadar Kuba a Najeriya, Clara Escandell ta kai masa ziyarar bangirma.

Mr. Runsewe yace:”kasashen biyu nada dimbin albarkatun al’adu da yayi kama da Juan musamman a bangaren kade-kade da raye-raye da zai basu damar.”

Babban Darektan ya kuma ce ”cibiyar NCAC ta samar da hanyoyi ga al’momi a bangaren Diflomasiya ta yadda zasu rinka musayar raayoyin da suka shafi al’adu.”

Mr. Runsewe ya kara da cewa bukin kasuwar baje kolin kasa da kasa na bana, INAC, ya tara al’uma daga kasashen duniya daban daban

.Runsewe yayi alkawarin wannan baje kolin na bana zai baiwa Janhuriyar Kuba dama ga hamshakan mutane da su tattauna da manema labarai ta hanyar samar wa matasa hanyoyin musayar raayoyin al’adun su.

Yabo

Runsewe ya yaba da irin shigar kayan gargajiyar ‘yan Najeriya da Jakada Escandell tayi kuma yayi alkawarin kai ziyara Kuba nan bada jimawa ba.

LADAN NASIDI

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *