Hukumar kula da Jin dadin alhazai ta jahar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya ta ce maniyata aikin hajjin Shekara ta 2023 zasu biya naira Miliyan biyu da dubu Dari biyar kamar yadda aka biya a baya a matsayin kudin ajiya na aikin hajjin kafin a kaiga samun cikakken bayani daga hukumar aikin Hajji ta kasa wato NAHCON
Shugaban hukumar Alhaji Umar Makun Lapai shi ne ya bayana hakan jim kadan bayan kammala taro da masu ruwa da tsaki inda aka yi bitar aikin hajjin shekarar da ya gabata don sanin inda za a daura a ci gaba da shirye shiryen fara aikin hajjin Shekara mai kamawa
Alhaji Umar Makun Lapai ya ce maniyata za su biya kudin ne ta hanyoyin da aka tsara ta hanyar adashen gata ta hanyar biya kadan kadan ko Kuma ta biya a dunkule ta bankunan da hukumar aikin Haji ta kasa NAHCON ta amince da su.
Shugaban hukumar ya ce hukumar zata bayyana adadin kujerun kowace karamar hukuma da zarar an sami cikakkun bayanai na yawan kujerun da aka warewa jahar Neja a aikin hajjin bana.
” Duk irin matsayin da NAHCON ta dauka shi ne zai fayyace yawan kujerun da kowace karamar hukuma za ta samu, inda hukumar ke da karfin daukan kujeru dubu biyar, inda Kuma muke dakun amincewar sauran bukatun mu da muka nema a hannun gwamnatin jaha.”
Hukumar Jin dadin alhazan ta jahar Neja bisa irin yadda ta gudanar da ayyukan ta a aikin hajin bara ta Sami lambar Yabo daga kungiyoyi daban daban ciki harda kungiyar wakilan kafafen yada Labarai dake dauko rahotan aikin haji wato Haj Reports.
Ak
Leave a Reply