Take a fresh look at your lifestyle.

Rundunar Yandan Neja Ta Karyata Kai Harin Ta’addanci Kan Sojoji

Nura Mohammed, Neja

0 184

Rudunar yan sandan Jahar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya ta karyata Labarin dake yawo a kafafen sadarwa na zamani inda yake nuni da cewar Yan bindiga sun kaiwa dakarun sojan Dake kula da shingen bincike a kusa da Zuma Rock hari da Kuma yadda  a ke samun kwararar yan bindigan daga yankin Birnin Gwari a jahar Kaduna zuwa jahar Neja.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rudunar Yan sandan a Jahar Nejan DSP Wasiu Abiodun ya fitar, ya bayana cewar rahotan karyan ya nuna yadda aka sanya dokar hana fita na tsawon sa’oi 24 a yankin Kagara, inda ya ce ba wani rahoto daga jami’in dan sandan dake kula da yankin DPO ko daga bangaran hukumar tsaron farin kaya ta DSS a karamar hukumar Rafi, kana Kuma ba wani rahoto kan hakan a yankin na Zuma Rock da ke karamar hukumar Suleja.

A don haka kwamishinan Yan sanda jahar Neja CP Ogundele Ayodeji ya bukaci alumma da su Yi watsi da rahotan kana su cigaba da harkokin su na yau da kullum ba tare da tsoro ba , ya Kuma bukaci alumma da su taimakawa rudunar Yan sandan tare da sauran jami’an tsaro da sahihin bayanai don ganin an magance irin wadannan matsalolin na samun labaran karya a cikin alumma.

Ak

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *