Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Buhari Ya Nemi Halalta Shirin Sa Jari Na Jama’a

Aliyu Bello Mohammed, Katsina

0 430

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rubutawa majalisar dattawa wasika, yana neman halastawa tare da kafa tsarin zuba jari a Najeriya NSIP.

 

Wannan dai na daya daga cikin bukatun da aka mikawa majalisar dattawan a ranar Talata ta wasiku daban-daban da shugaban majalisar dattawan Najeriya Ahmad Lawan ya karanta.

 

Shugaba Buhari kan shirin zuba jari na zamantakewa ya bukaci majalisar dattijai ta yi nazari tare da amincewa da wani kudurin doka don kafa shirin.

 

Ya bayyana a cikin wasikar wadda shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya karanta, cewa yin nazari da kuma amincewa da kudirin zai samar da dokar da za ta ba da damar aiwatar da shirin yadda ya kamata da nufin kawar da fatara da ‘yan Najeriya masu rauni.

 

A bangaren dajin na kasa kuwa, shugaba Buhari a wata wasika ya bukaci amincewar majalisar dattijai ta amince da dokar da aka yi a farkon shekarar nan na kafa sabbin wuraren shakatawa na kasa guda 10 a fadin kasar nan.

 

Shugaba Buhari a wasu bukatu biyu daban-daban na neman a duba tare da amincewa da dokar kafa Laburare ta Kasa 2022.

 

Dokar da aka gabatar a cewarsa za ta samar da tsarin doka na kula da dakin karatu na kasa ta Najeriya kamar yadda ake yi a duniya.

 

Wata bukata ta shugaba Buhari ga ‘yan majalisar tarayya ta ta’allaka ne kan yin nazari tare da zartar da wani kudurin doka na hukumar binciken kayayyakin da ake sarrafawa ta tarayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *