Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Litinin din da ta gabata ya jaddada aniyarsa na mika ragamar mulki ga zababben shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayun shekara mai zuwa 2023, yana mai cewa wa’adin mulkin sa zai kare a wannan rana kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
A wani takaitaccen jawabi ga Mista Shakib Ben Musa, Ministan Ilimi na Kasa, Makarantu da Wasanni na Masarautar Morocco wanda ya ziyarci fadar gwamnati a matsayin manzon na musamman kare da bikin rantsar da sabon shugaban kasa a watan Mayun badi.
Sai dai ya ce zai yi nazari kan sakon da aka aiko tare da mayar da martani yadda ya kamata, tare da bayar da tabbacin a lokaci guda zai ci gaba da kula da karfafa kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Wakilin Masarautar Morocco a Najeriya, Mista Moha Ou Ali Tagma, wakilin na musamman ya sake jaddadawa shugaban kasar zumunci da hadin kan Sarki da gwamnati da al’ummar kasar Moroko da ‘yan Najeriya.
Leave a Reply