Gwamnatin jihar Legas ta jaddada kudirinta na tabbatar da samar da wutar lantarki mai dorewa ga daukacin mazauna jihar nan da shekara ta 2036.
Gwamnatin ta kuma jaddada bukatar hada hannu da masu zuba jari masu zaman kansu domin aiwatar da aikin ta hanyar rarraba makamashi.
Kwamishinan Makamashi na Jihar, Mista Olalere Odusote ne ya bayyana hakan a wajen taron baje koli na Kasuwar Gidaje na Legas karo na uku, wanda Hukumar Kula da Gidaje ta Jihar Legas, LASRERA ta shirya
Da yake magana kan batun; “Bayar da masana’antar gidaje ta jihar Legas ta hanyar bunkasar kasuwar makamashi a Legas, Kwamishinan ya ce daya daga cikin muhimman abubuwan da jihar ta mayar da hankali a kai shi ne ganin an cimma burin ci gaba mai dorewa na 7, wanda shi ne samar da isassun sararin samaniya mai dorewa.
Odusote ya jadadda cewa, jihar na zage damtse wajen ganin an samar da ababen more rayuwa da suka dace domin ciyar da al’umma da ke karuwa.
Odusote ya jadadda cewa, jihar na zage damtse wajen ganin an samar da ababen more rayuwa da suka dace domin ciyar da al’umma da ke karuwa.
”Don haka, Legas dole ne ta samar da ababen more rayuwa daga gidaje da makamashi yayin da muke fafutuka kan takaitaccen kasafin kudi don samar da wutar lantarki, lafiya, hanyoyi, gidaje, sufuri ga yawan jama’a, yana da ma’ana a fara duban hanyoyin samar da kudade.” Yace.
Leave a Reply