Rundunar Yan sandan Najeriya a Katsina ta tallafa wa Iyalan Jami’anta da suka rasu a bakin aiki
Kamilu Lawal,Katsina
Kwamishinan yan sandan jihar Katsina Shehu Nadada ya hannanta chakin Kudi na sama da Naira miliyan Hamsin da Hudu ga Iyalan jami’an rundunar da suka rasa ransu a baking aiki
Raba kudaden wani bangare ne daga cikin kudurin Babban sifeton yan sandan najeriya na jinkan Iyalan jami’an yan sanda a fadin najeriya
Da yake jawabi a wajen bikin mika kudaden ga Iyalan yansandan a shelkwatar rundunar a madadin Babban sifeton, Kwamishina Shehu Nadada ya bukaci wadanda suka karbi tallafin da suyi amfani da kudaden yadda ya kamata
Kwamishinan wanda ya jinjinama babban sifeton yansandan ya kuma tabbatar da cewa rundunar ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen inganta walwalar jami’anta dake kan aiki hadi da tallafama iyalan wadanda suka rasa ransu a bakin aikin
Yana mai cewa“Ina mai amfani da wannan dama in godema Allah in kuma yabama Babban sifeton yan sanda na kasa Usman Alkali Baba bisa wannan tausayawa ga Iyalan jami’anmu da suka sadaukar da rayuwar su wajen kokarin kare lafiya da dukiyoyin al’umma kasar nan”.
“A madadin Babban sifeton yan sanda Usman Baba nike gabatar da chakin kudi na Naira miliyan Hamsin da Hudu da dubu dari biyar da Talatin da Biyu da Naira Dari Tara da Tara da kwabo Talatin da Biyu.(54,532,909:32K) ga iyalai da magadan jami’anmu da suka sadaukar da ransu wajen kare martabar al’umma.
“Ina mai kira ga Iyalan da suka amfana da suyi amfani da kudaden wajen inganta rayuwar iyalai da magadan jami’an”, Inji Nadada
Ya bukaci al’ummar jihar da su rika tallafawa rundunar ta hanyar bata mahimman bayanai domin samun nasarar aikinta na kare lafiya da dukiyoyin al’umma.
Leave a Reply