SASHIN KULA DA AL’AMURAN MATA TA UN TA BUKACI HADIN KAN MATA A NAJERIYA
TIJJANI USMAN BELLO, Maiduguri.
A lokacin da take jawabi a yayin bude taron karawa juna sani na
kwaniki biyu, da sashin kula da al’amuran Mata ta Majalisar Dinkin
Duniya UN da hadin gwiwar wasu Kungiyoyi suka shiryawa Mata ‘Yan
takarar Mukamai a jam’iyyu daban-daban, da aka gudanar dashi a garin
Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno dake Arewa Maso gabashin
Najeriya.
Bubban Jami’a a sashin kula da hakkin Matar a Najeriya, Uwargida
Emmanuela Azu, ta ce,’’Samun hadin kan Mata a tsakaninsu yana daya
daga cikin samun nasarar Mace ta a halin Karatu, Siyasa, Aikin
Gwamnati da wasu al’amuran yau da kullum, a don haka wajibine ku hada
kawunanku ku zama tsintsiya madaurinki daya, da manufa daya, sannanne
zaku samu nasara tare da ci gaba.’’
Ta ce,’’ Ba muna cewa Mata su yi kafada da kafada da Mazabane, amma
dai muna kokarin fahimtar da Mutanene su fahimci irin taimakon da
Uwargida take yima Maigidane wajen tafiyar da harkokin gida,
musanmamma a tafiyar da rayuwar Yara, a don haka wajibine Mata su mike
tsaye wajen neman ilimi, tsunduma cikin siyasa, da neman Mukaman
gwamnati don taimakawa Iyalai, domin a wani lokacin Maigida zai iya
gajiyawa, to amma idan Mata tana da wani abinyi to zata iya taimakawa
gida.’’
A kasidar da ta gabatar a wajen taron Shehin Malama a Tsangayar
Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Maiduguri Uwargida Patricia Donly, ta tabo
muhimmancin baiwa Mata taka rawa a fagen Siyasa,
‘’Baiwa Mata
dama su taka rawa a fagen Siyasa yana da muhimmanci matuka gaya, domin
zata iya cike gurbin daman da Mata suke samu a wasu wuraren, kuma zata
iya taimakawa Mata ‘yan uwanta da Maigida da Yara a cikin gida, a don
haka maganar ace a hanawa Mata rawar takawa a wannan zamanin abune
wanda yake da matsanancin wahala ga su kansu Matan, a don haka muna
kira ga alumma su fahimci abin da muke nufi na shigar da kashin Mata
cikin gwagwarmayar Siyasa ko ilimi, da sauran harkokin rayuwa.’’
Itama a kasidar da ta gabatar mai karfafawa Mata karfin gwiwa Malama
Maimuna Garba, Ma’aikaciya a Hukumar Gidan Talabijin ta Kasa NTA a
Maiduguri, ta ce ‘’Mata wajibine Mata ku cire tsoro, kuma kasance
masu kwarin gwiwa da kyakkyawar zato, sannan kuma ku cire kyashi da
bakin ciki a tsakaninku.’’
Ita ko ‘Yar takarar gwamna a karkashin tutar jam’iyyar ADC, Malama
Fatuma Abubakar, ‘’Na tsaya wannan takarane don in tsamar da
Matasanmu daga shiga munanan Dabi’u, in kuma yi kokarin samar da
aikinyi gas u kansu Matasan da suka kammala Makaranta, don dogaro da
kai, sannan kuma zan kafa kananan Masana’antu da inganta samar da
wutar lantarki, don inganta kananan Masana’antun, sannan kuma zanyi
kokarin inganta harkar ilimi da kiwon lafiya, in har na samu daman
darewa wannan kujera, in jita.
‘Yan takara daga mukamai daban-dabanne
a maban-banta jam’iyyune suka halarci taron karawa juna sanin da aka
gudanar dashi a garin Maidugurin.
Leave a Reply