Take a fresh look at your lifestyle.

Mazauna Jihar Nasarawa Sun Yaba Da Aikin Titin Gwamnatin Tarayya A Jihar Nasarawa

Theresa Peter

0 201

Mazauna karamar hukumar Keffi da ke jihar Nasarawa a arewa ta tsakiyar Najeriya sun yabawa gwamnatin tarayya bisa sauri da ingancin hanyar Keffi zuwa Lafia wanda a halin yanzu ke tafiya kuma ake sa ran kammala shi a farkon shekarar 2023.

 

A wata hira da manema labarai, sun ce kamfanin da ke aikin gina hanyar, China Harbor Engineering Company (CHEC) ba kawai yana yin aiki mai inganci ba, har ma yana daukar nauyin da ya rataya a wuyansa na zamantakewar jama’a.

 

Hakazalika jama’ar sun yaba da kokarin ma’aikatar ayyuka karkashin jagorancin minista Babatunde Fashola bisa jajircewarsa wajen ganin an samar da aikin titin da zai amfanar da al’ummar jihar ta fuskar bunkasar tattalin arziki da ci gaban kasa.

 

Wani shugaba mai suna Mohammed Agwai, ya yabawa kamfanin na CHEC bisa yadda yake gudanar da ayyukansa tare da yin kira ga sauran kamfanonin gine-gine da su yi koyi da shi a wuraren da suke gudanar da ayyukansu a fadin Najeriya.

 

“Muna da sako ga Ministan Ayyuka, Babatunde Fashola. Yana yin aiki mai ban mamaki. Mun san cewa za a kammala wannan aikin kuma a kai ga jama’a. Muna mika godiyarmu ga gwamnati kan yadda ta inganta rayuwarmu,” inji shi.

 

Wani jigo a garin Keffi, Alhaji Sefiu Rafiu wanda shi ma mai cike da godiya ga gwamnati ya ce tun lokacin da gwamnati mai ci ta fara gina hanyar, mazauna yankin sun ci gajiyar wannan hanya ko kuma wata hanyar da kamfanin gine-ginen ya dauki wasu daga cikinsu aiki.

 

“Wannan hanya ta kasance abin tsoro tsawon shekaru. Mun sami matsaloli da yawa a wannan hanya. Cunkoso, zirga-zirga, wani lokacin zirga-zirgar yakan wuce tsawon yini guda. Amma mun ji dadi a yanzu, wannan hanyar tana tafiya da sauri, kuma mun ji dadin gwamnati da kamfanin gine-gine. Suna da abokantaka sosai Ba mu taba samun matsala da su ba,” ya kara da cewa.

 

Alhaji Rafiu ya sake jaddada bukatar daukacin kamfanonin gine-gine a Najeriya da su sa hannu a ayyukan kamfanoni a cikin al’ummominsu daban-daban, musamman ta fannin ayyukan yi.

 

Ya kuma yabawa CHEC bisa yadda take yin tasiri ga al’ummar Keffi ta hanyar daukar matasansu aikin yi domin yawancin ma’aikatansu ‘yan asalin jihar Nasarawa ne wanda ya inganta tattalin arzikin al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *