Take a fresh look at your lifestyle.

Sama da mutane 500 a jihar Katsina suka amfana ta shirin inganta rayuwar al’umma na NG-CARES

KAMILU LAWAL,Katsina.

0 264

Kimanin , mutane 516 ne suka shiga kuma suka amfana da tallafi, a karon farko na shirin Farfaɗowa daga Illar Tattalin Arzikin da Cutar Korona ta Haddasa a Tarayyar Najeriya – NG-CARES don inganta rayuwar al’umma.

 

 

Jami’ar Shirin, Mai Kula da Sashen Inganta Rayuwar Al’umma, a ƙarƙashin Hukumar Bunƙasa Rayuwar Al’umma ta CSDA, Hajiya Jummai Garba ce ta sanar da haka a lokacin da take tattaunawa da Mahukuntan Ofishin Tattara Bayanai na Mutane Marasa Ƙarfi na Jihar Katsina, watau SOCU.

 

 

Wannan yana ƙunshe a wata sanarwa da Jami’in Sadarwa da Samar da Bayanai na Ofishin Tattara Bayanan Marasa Ƙarfi, Marwana Abubakar Darma ya raba wa manema labarai a Katsina.

 

Sanarwar ta yi nuni da cewa an tsamo mutanen da suka amfana daga Kundin Tattara bayanai na Jihar Katsina – Social Register – wanda Ofishin na SOCU ya samar.

 

 

Hajiya Jummai Garba ta ƙara da cewa, gidajen Masu Ƙaramin Ƙarfi 1,030 ne daga cikin

1,280 aka tantance, a yayin da, tuni mutane 516 da aka zaɓo, suka karɓi katinansu na karɓar kuɗaɗe – ATM.

 

Ta bayyana cewa mata da matasa da suka amfana da shirin,  sun fito ne daga Ƙananan Hukumomin Daura, Dutsinma, Faskari, Kankara, Kafur da Jibia, kuma sun karɓi tallafi na tsakanin Naira dubu Arba’in da biyar zuwa hamsin don bunƙasa ƙanana da matsaƙaitan sana’o’insu da annobar cutar Korona ta kassara.

 

Jami’ar, ta ƙara da cewa, ana fatan ƙara yawan kuɗaɗen da ake bayarwa tallafi a karo na gaba ga waɗanda za su amfana daga Kundin Mutane Marasa Ƙarfi na Jihar nan.

 

Da yake mayar da jawabi, Shugaban Shirin Tattara Bayanan Mutane Marasa Ƙarfi mai riƙon ƙwarya, Alhaji Kabir Adamu wanda ya gode wa Jami’ar bisa wannan ziyara, ya bayyana wannan yunƙuri a matsayin ci gaba.

 

Ya ce ƙofa za ta cigaba da kasancewa a ɓuɗe ga masu buƙatar tallafawa ga Marasa Ƙarfi a jihar, musamman daga ƙungiyoyin bada tallafi da gwanmatoci, yana mai jaddada cewa, Kundin, za ya zama marar alfanu, muddin ba a yi amfani da shi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *