Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranci taron Majalisar Zartaswa a ranar Laraba.
Ana gudanar da taron Majalisar zartaswar ne a fadar Shugaban kasa dake,babban birnin tarayya, Abuja.
Daga cikin wadanda suka halarci taron har da Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; Hadimin Shugaban kasa, Farfesa. Ibrahim Gambari; da Sakataren din din din a gidan gwamnati, State House, Umar Tijani.
Ministocin da suka samu halatar taron Majalisar na ranar laraba sun hada da na Kimiya da Fasaha, Ogbonnaya Onu; Harkokin Wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama; Yada labarai da al’adu, Lai Mohammed; Babban birnin tarayya Mohammed Bello, MakamashiMuazu Sambo; Masanaantu, Ciniki da saka Jari, Niyi Adebayo; da Wasanni da ci gaban Matasa, Sunday Dare.
Sauran wadanda suka halarci taron majalisar zartaswar akwai Ministan kasa na Maaikatar kimiya da Fasaha, Hassan Abdullahi; Makamashi Jedy Agba; da na aiyyuka da gidaje, Abubakar Aliyu.
Sauran Mambobin Majaliisar zartaswar sun samu halarta ta yanara Gizo daga ofisoshin su.
LADAN NASIDI
Leave a Reply