Garambawul din da akayi a hukumar ya biyo bayan sanya hannun da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi sakamakon kare waadin tsofaffin Mambobin ta.
AIn jawabin da Ministan yada labarai da al’adu Alhaji Lai Muhammed ya fitar,yace Honorabul Bashir Omolaja Bolorinwa shine Shugaban Hukumar Kula da harkokin ta.
Sauran mambobin sun hada da jigajigan mutane, akwai Mr. Wada Asab Ibrahim, Mr. Iheanyichukwu Azubike Dike, Mrs. Adesola Oyinloye Ndu da kuma Mr. Olaniyan Olatunji Badmus.
Hakazalika akwai Mr. Bashir Ibrahim, Mr. Obiora Ilo, Mr, Ahmad Sajo, Engr. Bayo Erikitola, wakilin hukumar farin kaya, wakilin Maaikatar yada labarai da al’adu da kuma Babban Shugaban Hukumar ta NBC.
Shekara uku ne kacal tsawon da mambobin zasuyi a bakin aiki.
LADAN NASIDI
Leave a Reply