Take a fresh look at your lifestyle.

An fara anfani da Sabbin Takardun Naira

Aisha Yahaya

0 195

Sabbin takardun Naira da aka yi wa kwaskwarima a Najeriya yanzu sun fara yawo yayin da bankunan Deposit Money a yau suka fara raba wa kwastomominsu kudaden ta hanyar biya ta kan layi.

 

Wannan na zuwa ne makonni uku bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabbin kudirorin a taron majalisar zartaswa ta tarayya na mako-mako.

 

Sabbin takardar kudin Naira da aka sake fasalin na cikin takardun kudi N200, N500 da N1,000.

 

A cikin wasu abubuwa, ana sa ran takardun da aka sake fasalin za su taimaka wajen kawar da kudaden da ke wajen bangaren banki da kuma dakile kudaden jabun.

 

A watan Oktoba ne Babban Bankin Najeriya ya sanar da cewa babban bankin zai sake fitar da wasu takardun kudi na Naira nan da ranar 15 ga Disamba, 2022, tare da bayyana cewa za a daina daukar tsofaffin takardun a matsayin takardar kudi kafin ranar 31 ga Janairu, 2023.

 

Ko da yake dai wasu sukar da suka biyo bayan sanarwar da bayyana takardun da kuma wa’adin da aka diba a kan tsofaffin takardun kudi, gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya ce babu ja da baya kan janye tsoffin takardun da kuma kaddamar da sabbin kudaden.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *