Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dawo Abuja bayan halartar taron shugabannin kasashen Amurka da Afirka.
Shugaba Buhari, wanda ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja ya samu tarba daga karamar ministar babban birnin tarayya, Ramatu Tijjani, Sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali da shugabannin sauran hukumomin tsaro.
Shugaban na Najeriya dai ya tafi birnin Washington DC domin halartar taron da gwamnatin Amurka ta shirya wa shugabannin kasashen Afirka.
A wajen taron, shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya yabawa shugaba Buhari kan zurfafa dimokaradiyya a Najeriya da Afirka.
Ya kuma bukaci kasashen Afirka da za su gudanar da zabe a shekara mai zuwa, da su tabbatar an gudanar da zabe cikin gaskiya da lumana.
Shugaba Buhari ya yi amfani da wannan damar wajen jawo hankalin masu zuba jari na Amurka zuwa Najeriya, inda ya ba su tabbacin cewa yanayin ya dace da su don yin kasuwanci.
Leave a Reply