A Tunisiya shugaban kasar Kais Saied ya kada kuri’arsa a wata rumfar zabe da ke cikin wata makarantar firamare a babban birnin kasar Tunis.
Al’ummar Tunisia na kada kuri’a a zaben ‘yan majalisar dokokin kasar domin zabar wakilansu a majalisar mai kujeru 166.
Da yake jawabi bayan kada kuri’arsa, Saied ya tunatar da ‘yan takarar irin nauyin da ke wuyansu.
“Su wadanda za a zabe a yau ko a zagaye na biyu, su tuna cewa za su kasance karkashin sa idon masu kada kuri’a, don haka idan suka koma kan wadanda suka zabe su ba su yi aiki ba. a gaskiya su kawo abin da suka alkawarta wa masu zabensu, mai yiyuwa ne a janye wa’adinsu, kamar yadda dokar zabe ta tanada”, in ji shugaban na Tunisiya.
Jam’iyyun siyasa na adawa sun yi kira da a kauracewa zaben.
Sun ce wannan zabe wani bangare ne na abin da suka bayyana a matsayin “juyin mulki” ga dimokradiyya tare da yin tir da rashin ikon majalisar.
Tunisiya na cikin matakin karshe na tattaunawa kan shirin ceto kusan dala biliyan biyu daga asusun lamuni na duniya IMF don ceto kudaden al’ummarta da ke fama da rikici.
Leave a Reply