Sabuwar Hukumar Binciken Hadura ta Najeriya (NSIB) ta fitar da rahotannin hadurra guda bakwai.
Sabbin rahotannin da hukumar ta fitar sun bayar da rahoton hadurran jiragen sama guda 82 da hukumar ta fitar tun bayan kafata a shekarar 2007 da jimillar rahotanni 63 da gwamnati mai ci ta fitar daga shekarar 2017 zuwa yau.
Rahoton ya hada da lamarin da ya shafi Jirgi mai saukar Ungulu na Kanfanin Bristow, jirgin Embraer 135 mai lamba 5N-BSN, wanda ya faru a filin jirgin sama na soja na Fatakwal (NAF BASE), Fatakwal, ranar 9 ga Maris, 2020.
Sauran sun hada da jirgin ATR-72 mai lamba 5N-BPG, mallakar kamfanin Overland Airways Limited a filin jirgin sama na Ilorin, ranar 29 ga Nuwamba, 2014, jirgin Boeing 737-300 na Air Peace Limited mai lamba 5N-BUO a FL310 akan hanyar shi ta uwa Enugu daga Legas a ranar 14 ga Disamba, 2018, da jirgin British Aerospace BAE 125-800B mai lamba 5N-BOO, a Fatakwal, Najeriya ranar 16 ga Yuli, 2020.
Har ila yau, an samu rahoton faruwar al’amura da suka shafi jirgin British Aerospace BAE 125-800B mai lamba 5N-BOO karkashin Gyro Aviation Limited, a filin jirgin Osubi, Warri, a ranar 10 ga Satumba, 2020, wani jirgin Dornier 328-100 mai lamba 5N-DOX, na Najeriya Dornier. AIEP (DANA) Limited, a filin jirgin saman soja na Port Harcourt a ranar 23 ga Janairu 2019 da Airbus 330-243 na Middle East Airlines mai lamba OD-MEA da fakin jirgin Boeing 777 na Turkish Airlines mai alamar TC-LJC a filin jirgin saman Murtala Mohammed. Legas a ranar 29 ga Yuli, 2020.
Ofishin ya kuma fitar da jimillar shawarwarin kiyaye hadura dari biyu da saba’in da biyu tun daga lokacin da aka kafa ta tare da shawarwari dari da casa’in da daya daga cikin shawarwarin da wannan gwamnati ta fitar.
Kwamishinan ya ce a yanzu hukumar tana da hurumin binciken hadurran kan tituna, hadurran jiragen kasa da hadurran teku, ciki har da na Sararrinb sama wanda shi ne babban aikinta.
“Yayin da aka fadada aikin hukumar a yanzu zuwa wasu sassa, za mu tura karin Maaikata, kayan aiki na zamani don gudanar da ayyukanmu cikin sauki domin mu yi wa kasa hidima da kuma cika ka’idojin kasa da kasa.”
Kwamishinan ya ce ofishin ya ci gaba da jajircewa, ta hanyar inganta matakai, iya aiki da kayan aiki, don cika aikin yadda ya kamata, da manufa da kuma kwarewa.
Leave a Reply