Take a fresh look at your lifestyle.

Rundunar ‘Yan sandan Najeriya ta yaye ‘yan sanda 455 a jihar Neja

0 108

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yaye jami’an ‘yan sanda sama da 455 a Kwalejin horas da ‘yan sanda da ke Minna a Jihar Neja dake Arewa ta Tsakiyar Najeriya.

 

 

‘Yan sandan sun hada da 369 daga jihar Neja da 86 daga babban birnin tarayya Abuja.

 

 

Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda AIG Kayode Egbetokun, AIG Shiya ta 7 ne ya wakilci Sufeto Janar na ‘yan sanda, Alkali Baba a wajen faretin.

DSP Wasiu Abiodun, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, yace sun samu horo na tsawon watanni shida a makarantar horo.

 

 

 

Bikin ya samu halartar Gwamnan Jihar Neja Alh. (Dr.) Abubakar Sani Bello, Sakataren gwamnatin jiha Alh. Ahmed Ibrahim Matane.

 

 

Sauran manyan baki da suka halarci taron sun hada da kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja, CP Ogundele, shugabannin sauran hukumomin tsaro, ‘yan majalisar dokokin jihar Neja, Hon. Abdul-Malik Sarkindaji, tsohon kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, manyan jami’an rundunar da sauran manyan baki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *