Uwargidan gwamnan jihar Legas, Dakta (Mrs) Claudiana Ibijoke Sanwo-Olu, ta jaddada kudirin ta na karfafa wa gwamnatin jihar aiwatar da tsare-tsare da a kula da lafiyar mata da kananan yara don dakile mace-macen mata, yara da jarirai.
Misis Sanwo-olu ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadin da ta gabata yayin da take maraba da sabuwar shekarar jariran da aka haifa a asibitoci uku mallakar jihar.
Uwargidan gwamnan ta kuma bayar da kayayyaki kyauta ga jariran farkon shekara da aka haifa a cibiyar Maternal Child Center Eti-Osa, Babban Asibitin Ebute-Metta da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Legas, Ikeja.
A cewar sanarwar, Jariri Ayinde, namiji mai nauyin kilogiram 3.1, wanda Misis Ayinde ta haifa da misalin karfe 12:01 na safe, shine jariri na farko a wannan shekara a cibiyar kula da mata masu juna biyu ta Eti-Osa. Jaririya Iromain, ita ce wadda nauyinta ya kai kilogiram 2.9 kuma an haife ta da karfe 12:02 na safe,Misis Olufoye ta haifi ‘yan uku ta hanyar tiyatar cire su. An haifi yaron farko mai nauyin kilogiram 2.2 da misalin karfe 12:07 na safe; Yaro na biyu, namiji mai nauyin kilogiram 2 an haife shi da karfe 12:08 na safe yayin da yaro na uku, mai nauyin kilo 2.1 an haife shi da karfe 12:09 na safe.
Da yake maraba da jariran farko a wadannan asibitocin, Sanwo-Olu ya ce tarbar jarirai wata alama ce mai matukar muhimmanci da ke ba da tabbacin cewa ana ci gaba da gudanar da al’adun bil’adama.
Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin jihar Legas ta hannun ma’aikatar lafiya, ta ci gaba da gudanar da ayyukanta na samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga daukacin mazauna jihar, kuma har yanzu tana kan shirye-shiryen dakile mace-macen mata masu juna biyu.
Uwargidan Gwamna tace gwamnatin jihar Legas ta aiwatar da tsare-tsare da dabaru da ya taimaka wajen inganta lafiyar mata da kananan yara a jihar, ta kara da cewa inganta da gina sabbin cibiyoyin kula da mata da kananan yara da samar da ayyukan yi an tsara su ne domin rage yawan mace-macen mata da yara ‘yan kasa da shekaru biyar a jihar.
Ta ce, “Ina so in yaba wa ma’aikatar lafiya bisa ci gaba da inganta ababen more rayuwa; samar da kayan aiki masu dacewa, canji mai kyau ga ma’aikatanmu, da Inganta aikin su, duk suna haifar da wani ma’auni na inganci da tasiri da gamsar da aboan aiki.
“Ina mai farin cikin ganin irin namijin kokarin da Hukumar Kula da Asibitin ke yi wajen samar da yanayi mai kyau da kwanciyar hankali a bangaren ayyukan kiwon lafiya a wadannan asibitoci.”
A yayin da take taya iyayen jariran murna, Uwargidan Gwamna ta yaba da kokarin daidaikun mutane da kungiyoyi masu ruwa da tsaki a duk wani nau’i na hadin gwiwa wajen ganin an cimma manufa da kokarin gwamnatin jihar a fannin kiwon lafiya tare da rokon sauran al’uma su shigo domin bada tasu gudumowar yin tasiri a cikin rayuwar iyalai. Ta kuma yi addu’ar Allah ya ba wa jariran da aka haifa lafiya da tsawon rai domin su girma su zama ‘yan kasa da kasa masu amfani.
A nasa jawabin, kwamishinan lafiya na jihar, Farfesa Akin Abayomi ya yaba wa Uwargidan gwamnan jihar Legas, bisa yadda ta ci gaba da gudanar da bikin baje kolin jarumai na farko na shekara, inda ta kara da cewa gwamnatin jihar na goyon baya sosai tare da jajircewa wajen kyautata rayuwar iyaye mata da Kananan yara, musamman ta fuskar kiwon lafiya mai inganci, da kuma isar da sako a jihar Legas. Ta kuma yaba wa gwamnati mai ci a karkashin jagorancin Mista Babajide Sanwo-Olu,irin kididdigar da ake da ita ta nuna cewa kididdigar kula da lafiyar mata da kananan yara a Legas ta inganta.
Leave a Reply