Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamna Tambuwal Ya Sha Alwashin Kammala Ayyukan Da Yake Yi Kafin Wa’adin Mulkin Shi

Hadiza Halliru, Sokoto

0 457

Gwamnan jihar Sakkwato kuma Babban Direktan yakin Neman zaben shugaban kasa na jam’iyar PDP, Aminu Tambuwal ya bukaci yan’siyasa da su kiyaye daukar makamai, domin samun hadin kai da gudanar da zabe a cikin lumana.

Gwamnan ya kuma bada tabbacin kammala ayyukan da suka rage kafin cikar wadinsa.

Tambuwal ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a fadar Gwamnatin jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya.

A cewarsa “kamar yadda muka sani jahohin Najeriya na bukatar yanayin zaman lafiya, wasu yankunan mu na fama da rashin tsaro ya kamata a tausayawa wadanda lamarin ya shafa ba a kara ta’azzara lamarin ba”.

Ya kuma ce jam’iyyar PDP jam’iyya ce mai bin doka da oda, inda take tafiyar da yakin neman zaben da babu kiyayya a ciki.

Gwamna Tambuwal ya bayyana dalilin jinkirta gudanar da karatu a makarantar Gudu, domin itace karamar hukuma daya tilo a Najeriya da ba ta da makantar sakandare.
“makarantar Gudu makaranta ce da nake matukar so a zuciyata amman abin takaici rashin tsaro ya hana mu shiga wurin, burina ne kafin in bar ofis mu shigar da dalibai a kwallejin, idan lamarin ya lafa, idan kuma bai lafa ba bazan kai yaron kowa ba a wurin, ina da tabbacin gwamnati mai zuwa zata yi nata ko kari,” in ji shi

Da yake magana kan sauran ayyukan da Gwamnatinsa ta gudanar yace lokacin da aka fara wadannan ayyuka babu ko daya daga cikinsu da aka yi watsi dasu.

Gwamna ya bada tabbacin kammala ayyukan da suka rage kafin cikar wa’adinsa.

 

Abdulkarim Rabiu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *