Gwamnan jihar Oyo dake kudu maso yammacin Najeriya, Seyi Makinde, ya bayyana jin dadin shi ga al’ummar jihar Oyo bisa gata da suka samu na yi musu hidima a cikin watanni 43 da suka gabata, inda ya bayyana cewa shekaru uku da watanni bakwai da suka gabata sun zama shaida na jajircewar shi da hidimar da yayi wa ‘yan jihar.
Gwamnan wanda ya bayyana hakan a cikin sakonsa na sabuwar shekara ga al’ummar jihar, ya bayyana cewa bai yi anfani da goyon bayan da aka baiwa gwamnatinsa a shekarun da suka gabata ba.
Ya ce: “Ba don umarni da goyon bayanku ba, da ba mu yi nasarar dora jiharmu mai daraja a kan turbar ci gaba mai dorewa ba. Dukkanin ayyukan da muka yi a karkashin tsarin samar da ci gaba a jihar Oyo a sekarar 2019-2023, ya yi tasiri.”
Makinde, wanda ya ci gaba da cewa gwamnatinsa ta samu damar nunawa jama’a cewa mai yiwuwa ne a mai da hankali wajen samar da ababen more rayuwa, yayin da a lokaci guda kuma ya cika wasu ayyukan jama’a da ya rataya a wuyan shi, wanda hakan ya bashi kwarin gwiwar cewa za a sake zaben shi a wani wa’adi na shekaru hudu a ranar 11 ga Maris, 2023, yace gwamnatin shi Zata dora jihar a kan turbar ci gaba mai dorewa.
Ya bayyana wasu nasarorin da gwamnatin shi ta samu a sassa daban-daban da suka hada da samar da ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, tsaro da fadada tattalin arziki da dai sauransu.
“A cikin kwata na farko na shekarar 2022, mun kammala tare da kaddamar da titin Garin Saki mai tsawon kilomita 9.7 da hanyar Gedu-Oroki-Sabo-Asipa mai tsawon kilomita 5.2. Zuwa kwata na biyu mun mika motocin aiki guda 100 ga kungiyar Amotekun domin saukaka ayyukansu. Mun kuma cire takunkumin kara wa ma’aikatan gwamnati karin girma da gwamnatin da ta shude ta sanya, tare da kara wa ma’aikata karin girma,” inji Gwamna Makinde.
A ci gaba da batun jin dadin ma’aikatan, gwamnan ya bayyana yadda gwamnati ta aiwatar da biyan albashin ma’aikata na watanni 13 a shekara ta hudu a jere, tare da baiwa ‘yan fansho kudaden Kirsimeti, inda ya ce an dauki karin ma’aikata 500 a cikin hukumar tsaro ta Amotekun a jihar Oyo, daga cikin wasu nasarorin da gwamnatin ta samu.
Ya ci gaba da cewa: “Bugu da kari, mun kaddamar da tashar hawa motocin jigilar mutane ta Challenge, Ojoo tare da Omituntun, wanda ya kafa sabon tsarin sufuri a jihar Oyo. Mun kuma cika alkawarinmu na kaddamar da kasuwar Sasa da aka sake ginawa.
“A cikin kwata uku na shekarar 2022, mun kaddamar da babban asibitin da aka gyara tare da samar da kayan aiki a karamar hukumar Atisbo, mai nisan kilomita 7.2 na Barikin Idi Ape-Basorun-Akobo-Odogbo, da kuma aikin jigilar iskar gas mai tsawon mita 65 da gwamnatinmu ta gina. ” a cewar Makinde.
Gwamna Makinde ya kuma bayyana jin dadinsa da yadda gwamnatin shi ta samu damar tabbatar da daukaka darajar kwalejin ilimi ta Emmanuel Alayande dake Oyo zuwa jami’ar ilimi, inda ya ce gwamnatinsa ta nuna jin dadi ta wajen yanke shawara, kuma manufofinta sun kasance na ‘yan adam domin al’ummar jihar Oyo sune masu ruwa da tsaki a harkokin mulki.
Ya ce: “Wataƙila ba ko yaushe za mu daidaita ba, amma mun yarda da kura-kuranmu kuma mu gyara idan ya yiwu. Mun ji kuma mun koya daga gare ku, don haka da gaba gaɗi mun komo zuwa gare ku, kuma mun nemi a sake yin wa’adi na biyu. Mun san cewa zuwa 11 ga Maris, 2023, za ku zabi Omituntun 2.0. Muna sa ran shekara mai ban sha’awa a gaba!”
Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya sa shekarar 2023 ta zama shekarar da gwamnatin shi za ta kafa ci gaba mai dorewa a jihar Oyo , tare da yi wa daukacin ‘yan kasa fatan 2023 mai albarka.
Leave a Reply