Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamna Ya Yi Allah-Wadai Da Kashe-Kashen da Kungiyar Asiri A Jihar Anambra Tayi

Aisha Yahaya, Lagos

0 141

Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, CFR ya yi Allah wadai da fada tsakanin kungiyoyin asiri da sukayi musayar wuta a Obosi da Okpuno a kananan hukumomin Idemili ta Arewa da Awka ta Kudu.

 

 

 

A garin Obosi, ‘yan adawar sun harbe shugaban karamar hukumar , Mista Ike Okolo a gidan mai a ranar Litinin, 2 ga watan Janairu, 2023, yayin da a harabar Obi Maduka da ke cikin dandalin garin Nodu Okpuno, Awka, ‘yan bindiga sun kashe Mutane hudu da aka bayyana sunayensu da Onyiebo Okoye, Kenechukwu Okeke, Jude Ebenezar da Obinna Maduka.

 

 

 

A wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Christian Aburime ya fitar, Gwamna Soludo ya yi Allah wadai da wadannan kashe-kashe na rashin hankali da kakkausar murya tare da bayar da tabbacin cewa za a kama wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da yanke hukunci mai tsauri ko da sun gudu daga garin.Ya jaddada cewa za’a farauto su domin fuskantar doka.

 

 

 

A wannan lokacin na bukukuwa, Anambra ta tayi kyakyawan bikin Kirsimeti a cikin shekaru da dama da suka wuce, domin babu zirga-zirga da sabon tsarin kula da zirga-zirgar ababen hawa da gwamnati ta yi a lokacin bukukuwan, inda matasa masu aikin sa kai na Anambara da hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar suka yi aiki a duk mahimman wurare don kula da zirga-zirga.

 

 

 

 

Gwamna Soludo ya kuma tabbatar da cewa ’yan kungiyar asiri da suka fafata a yau, tabbas za a bi su har maboya a kamo au a kuma hukunta su ta hanyar doka.

 

 

 

Ya yi kira ga al’ummar Anambara da sauran ‘yan Najeriya mazauna jihar da su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum dajin dadin kakar wasa ta bana domin kalubalen su ne kebantattun shari’o’in da za a fara shiga nan ba da dadewa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *