Take a fresh look at your lifestyle.

Rashin tsaro: Shugaba Buhari ya amince da tura manyan fasahohin zamani zuwa Kudu maso Gabas

0 253

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da tura na’urorin zamani na domin magance matsalar rashin tsaro a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

 

 

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar gwamnatin jihar bayan ganawar da yayi da shugaban kasar a fadar shugaban kasa dake Abuja ranar Talata.

 

 

Gwamnan ya ce ya zo ne domin ganin shugaban kasar da rokon ya amince da tura na’urorin fasahar Zamani ga yankin kudu maso gabas domin shawo kan kalubalen zaman lafiya da ke damun yankin.

 

 

A cewar shi, tare da amincewar shugaban kasar, nan ba da jimawa ba za a kai kayan aikin sa ido a yankin don shawo kan matsalar tsaro.

 

Ya kuma bayyana cewa ya kawo wa shugaban kasar ziyara ne a madadin al’umar shi, Uzodinma ya ce “kuma ya na godiya da irin goyon bayan da shugaban kasa ke bayarwa da kuma amincewa da mayar da Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya Owerri zuwa asibitin koyarwa na jami’a na Jami’ar Fasaha ta Tarayya. Hakanan, amincewar da ta mayar da Kwalejin Alvan Ikoku zuwa Kwalejin Ilimi ta Tarayya.

 

 

“Makonni biyu da suka wuce, ‘yan kabilar Igbo da suka dawo gida daga Legas da wajen Kudu maso Gabas sun ci gajiyar gadar Neja ta biyu abin da ya cancanci a yaba masa.

 

 

“Na kuma roke shi da ya tallafa mana da wasu ayyukan fasaha. Mun shirya za mu iya samar da kyakyawan tsaro a Kudu maso Gabas, Kuma ya yarda da haka.

 

 

“Daga yanzu, za mu sami wasu na’urorin sa ido da wasu fasahohin zamani wadanda za su taimaka mana wajen gudanar da tsaro ta yadda za mu iya yaki da aikata laifuka ba tare da wata illa ga muhalli ba.”

 

 

Ƙarin tabbacin ci gaba

 

Da yake ba da tabbacin jihar Imo a sabuwar shekara, ya bayyana cewa: “To, jama’ata ‘yan Nijeriya masu kishin kasa ne kuma mun yi imani da hadin kan kasar. Mun yi imanin zamu ci gaba a matsayinmu na al’umma, muna bukatar goyon baya da hadin kan gwamnatin tarayya. Saboda haka ci gaban da  za’a samu a shekarar 2023,sai ya ninka na shekarar bara 2022. Kuma za a inganta matakin ci gaban da muka gani daga 2020 zuwa 2022.

 

“Idan ka je Kudu maso Gabas misali a jihar Imo, mun samu amincewar shugaban kasa, wanda a yanzu ya baiwa gwamnatin jihar Imo da hadin gwiwar sojojin ruwan Najeriya damar ratsa kogin Oguta zuwa Kogin Orashi zuwa teku, wanda hakan ya sanya gwamnatin jihar Imo ta hada gwiwa da sojojin ruwan Najeriya suka bi ta teku suna buɗe hanyar teku. Sannan akwai wani sansanin sojan ruwa wanda ya kawo nasarar rugujewar laifuka tun lokacin da aka kafa shi”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *