Dan takarar gwamna na APC yayi alkawalin inganta rayuwar matasa da mata a jihar Katsina
Kamilu Lawal, Katsina
Dan takarar gwamnan jihar Katsina a jam’iyyar APC, Dr. Dikko Umar Radda ya bayyana kudurin sa na bunkasa hanyoyin samar da guraben aikin yi ga matasan jihar idan aka zabe shi ya zama gwamnan a zaben 2023 mai zuwa
Dr. Dikko Radda ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci karamar hukumar Katsina a cigaba da zagayen gangamin yakin neman zabe da yake gudanarwa a fadin jihar
Yace” Idan Allah yarda ya bani shugabancin jihar nan, matasan mu zasu samu aikin yi, matan mu zasu samu Sana’a”, inji Dikko Radda.
Dr. Radda ya kuma bayyana cewa zai inganta mahimman bangarorin cigaba irin su Ilmi da Noma da kiwon Lafiya da bangaren ciniki da masana’antu
“Zamu yima talakka gata ta hanyar rike amana domin inganta rayuwar ku”,dan takarar yace.
Dan takarar gwamnan wanda ya godema al’ummar yankin bisa kyakkyawar tarba da karbar da sukayi masa ya kuma bukace su da suyi amfani da katin zaben su yadda ya kamata su zabi jam’iyyar APC a dukkanin matakai
Da yake magana akan sha’anin tsaro, Dikko Radda yayi alkawalin amfani da matasa ta hanyar daukar su aiki tare da horar da su dabarun da suka wajaba domin kare yankunan su daga kalubalen tsaro
“Idan Allah ya bani nasarar zama gwamnan Katsina zan dauki matasa aiki a horar dasu dabaru domin yin aiki tare da jami’an tsaron kasa wajen yaki da yan ta’adda a yankunan jihar da matsalar tsaron tafi kamari”.
Yana mai cewa”yin hakan zai basu guraben aikin yi hadi da basu damar kare yankunan su ta hanyar fatattakar tsagerun da suka addabe su”, inji Dikko Radda.
Ya kuma bayyana kudurin sa na bunkasa bangaren aikin gona ta hanyar samar da sabbin dabaru da kayan aiki na zamani da nufin inganta sana’ar domin samun amfani mai riba
A dukkanin kananan hukumomin da ya ziyarta, dan takarar yana samun gagarumar tarba daga al’umma al’amarin da yake bayyana karbuwar sa ga al’umma jihar
A ziyarar gangamin yakin neman zaben da yake cigaba da gudarwa Dikko Radda yana tare da mataimakin takarar sa Farouk Jobe da shugaban jam’iyyar APC Alhaji Aliyu Sani da shugaban kwamitin yakin neman zaben dan takarar gwamnan, arch. Ahmad Dangiwa da masu takarar kujeru daban daban da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar ta APC.
Leave a Reply