Take a fresh look at your lifestyle.

Badakalar Sassan Jiki: An Kai Tsohuwar Mai Gidan Jana’iza Gidan Yari

Aisha Yahaya, Lagos

0 253

Megan Hess, mai shekaru 46 tsohuwar mai gidan ajiyar gawarwaki da Jana’izar su na Sunset Mesa kuma mai ba da agajin sassan jiki, an yanke mata hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari a ranar Talata saboda laifin damfarar ‘yan uwan ​​wadanda suka mutu da kuma sayar da sassan jikin ba tare da izini ba.

 

 

Da take amsa laifin zamba a watan Yulin 2022, Hess ta amince da lalata gawarwaki 560 da aka ajiye a inda take gudanar da kasuwancinta a wani gini dake Montrose, Colorado. A cewar kotun, mahaifiyarta mai shekaru 69, Shirley Koch, ita ma ta amsa laifin zamba, inda aka yanke mata daurin shekaru 15 saboda rawar da ta taka wajen farfasa gawarwakin.

 

 

“Hess da Koch sun yi amfani da gidan ajiyar gawarwaki su wajen satar gawarwaki da sassan jikinsu ta hanyar yin amfani da fom na jabun Kungiyar agaji. Halin nasu ya haifar da ɓacin rai ga iyalai da dangi, ”in ji mai gabatar da kara Tim Neff a kotu.

 

 

Wani bincike na Kanfanin Dillancin labaru na Reuters na 2016-2018 game da Cinikin sassan jikin Dan Adam a Amurka, sana’a ce da kusan ba ta da ka’ida, da ta haifar da shari’ar tarayya. Kuma Tsofaffin ma’aikatan bincike sun ce Hess da Koch sun yi anfani da sinadarin ajiyar gawa daga lalacewa ba tare da izini ba, kuma ‘yan makonni bayan da aka buga wani labari na 2018, FBI ta kai farmaki kan masu asuwancin.

 

 

A cikin bayanan kararrakin da aka shigar, Alkali jaddada yanayin damuwa akan irin halin da matar ta fada ya bayyana shi a matsayin daya daga cikin manyan laifukan tuammali da sassan dan adam a duk tarihin kasar Amurka. Kuma shekaru ashirin da aka yanke na ama gian yari an yi adalci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *