Cibiyar Kula Da Tsofaffi A Najeriya Ta Yaba Wa Shugaba Buhari Kan Kuduri Na Tsofaffi
Aisha Yahay, Lagos
Babban Darakta Janar na Cibiyar Kula da Tsofaffi ta Kasa (NSCC), Dakta Emem Omokaro, ya yaba wa kokarin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan nasarorin da aka samu kawo yanzu wajen magance matsalolin da suka shafi tsofaffi a Najeriya.
Omokaro, ya yaba wa shugaban kasar a ranar Talata a Abuja, ya ce ita ce gwamnati ta farko a tarihin Najeriya da ta Kyautata wa tsofaffi ta fuskar manufofi, tsarin shari’a, tsarin hukumomi da tsarin gine-gine.
“Wannan ita ce gwamnatin da ke tafiya a cikin Tsari, saboda haka za mu iya cewa da gaske, an sanya tsofaffin cibiayar NSCC cikin ayyukan ci gaban kasa.
“A halin yanzu, Cibiyar tana aiki tare da Ofishin hada kan shirye-shirye ta kasa (NASSCO), don samun Rajistar tsofaffi. Hakanan za a fitar da tsofaffi daga rajistar jama’a na gaba ɗaya.
“Wannan shi ne, zai tabbatar da cewa kaso mafi girma na tsofaffi sun ci gajiyar manufofin Gwamnatin Tarayya, hukumomin bayar da tallafi da kungiyoyi masu zaman kansu na kasa da kasa da sauransu.
“Har ila yau, ya dace a lura cewa Dokar Kariyar Tsaron Jama’a da aka sake fasali ta bar tsofaffi, amma yanzu ta haɗa su. Hakan na nufin akwai kyakkyawan fata ga tsofaffi a fadin kasar,” in ji Omokaro.
Shugaban NSCC ya yi bayanin cewa hukunce-hukuncen hukumar, sun yanke duk wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati, saboda haka, hadin gwiwa ya zama wani muhimmin abin da ake bukata na cikar ayyukan Cibiyar.
Ta ce cibiyar ta tashi tsaye wajen magance batutuwan da suka shafi kiwon lafiya, samun kudin shiga, tsaro da ‘yancin kai na kudi, musayar al’umma da jagoranci, cin zarafin tsofaffi, adalci ga tsofaffi da sauran su.
“Muna kuma da wani shiri mai suna ‘Grand Mother Tashi’. Amma don Allah a lura cewa ba na mata kawai ba ne.
“Ka sani, akwai ra’ayoyi da yawa game da Iyaye, wasu suna yi musu wani irin gani mara kyau,amma ba haka ba ne su ma Iyaye ne, amma idan ka lura da kyau, wadannan mutane suna yi wa al’ummarsu abubuwa da yawa amma ba a yarda da su ba.
“Shirin an yi shi ne, da nufin amincewa da matsayin kakanni da Iyaye a cikin al’umma sannan kuma yana kara kima ta hanyar hadin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki.
Omokaro ya bayyana cewa “Muna so mu samu amincewar sarakuna da ma malaman addini don tabbatar da cewa shirin Grand Mother Arise ya cimma burin da ake so a cimma ga tsofaffi a cikin al’ummomi daban-daban a fadin kasar.”
A cewar Omokaro, “ an samu dukkan wadannan ne, bisa kokarin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ministar jin kai, Hajiya Sadiya Umar Farouq.”
Leave a Reply