Take a fresh look at your lifestyle.

Aisha Yahaya,Lagos.

0 243

A karshen makon da ya gabata ne al’ummar yankin Isiokpo daga karamar hukumar Ikwerre na jihar Ribas a Kudancin Najeriya, suka shirya bikin kekuna na Isiokpo na shekara-shekara domin cikar shekara.

 

 

Bikin Carnival a Isiokpo shi ne bukin keke guda daya tilo a Najeriya kuma daya daga cikin manyan bukuwan carnival a yammacin Afirka.

 

 

Bikin Kekuna ya samu halartar ɗaruruwan mutane masu sanye da kayan gargajiya suna zagayawa cikin gari akan kekunansu don yin shagalin biki, inda ɗaruruwan ƴan kallo suka yi layi a kan tituna domin kallon masu keken a lokacin faretin kekuna.

 

Kara karantawa: Brazil ta yi bankwana da Pele tare da farkawa na awa 24

 

 

Yayin da wasu ke goye da fasinja , ana iya ganin wasu mahalarta taron ‘yan shekaru 70 zuwa 80 akan kekunan su ana yi musa tambayoyi daga gidajen Radio da Talabijin.

 

 

Ga al’ummar garin Isiokpo da ke Jihar Ribas, muhimmancin bikin shi ne nuna farin ciki da yadda jama’a ke amfani da kekuna na tsawon shekaru.

 

 

Har ya zuwa yau, an san ’yan kabilar Ikwerre da yin amfani da kekuna wajen safarar  kayan gonakinsu.

 

 

Makasudin bikin shi ne nuna kyawawan al’adun Najeriya ga duniya, tare da nishadantarwa da fatan alheri da tabbatar da kowa na cikin koshin lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *