Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya rattaba hannu kan wasu dokoki guda biyu domin bunkasa harkokin kiwon lafiya.
Hukumar ta kafa dokar Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe da kuma kafa Hukumar Kula da Lafiya ta Jihar Yobe.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Gwamna Buni, Alhaji Mamman Mohammed ya fitar.
Yace; “Dokokin biyu Zasu haɓaka samar da lafiya a akan haduran da suka hadurran cikin gida da na kan hanya, da kuma sa ido kan wuraren kiwon lafiya don samar da kyawawan ayyuka.”
“Dokar gudanar da aikin gaggawa na motar Asibiti .ta ba da damar jinyar agajin farko ga wadanda abin ya shafa daga wuraren da hatsarin ya faru kafin isa Asibiyi.
“Hakazalika, Hukumar Kula da Lafiya ta na baiwa hukumomin kiwon lafiya damar duba tare da lura da ayyukan da dukkanin cibiyoyin kiwon lafiya ke bayarwa a jihar don kawar da ayyukan da ba su da inganci da kuma hana tsangwama.
“Dokokin biyu za su tabbatar da cewa ba a tauye lamuran kiwon lafiya a kowane mataki a jihar Yobe,” in ji Mataimakin.
Tun da farko dai majalisar dokokin jihar ta zartar da dokokin.
Leave a Reply