Take a fresh look at your lifestyle.

Kakakin Majalisar Wakilai Yayi Bakin Cikin Rashin Farfesa Olotokun

0 318

Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila, ya bayyana mutuwar wani mashahurin masanin kimiyyar siyasa, Farfesa Ayo Olukotun a matsayin wani abin bakin ciki.

Mista Gbajabiamila ya ce Farfesa Olukotun dan Najeriya ne da ya ba da mafi kyawun ilimin sa don ci gaban kasar. Shugaban majalisar ya tuna yadda Farfesa Olukotun ya yi amfani da basirar da Allah ya ba shi wajen bayar da gudunmawa mai ma’ana ga gina kasa ta hanyar ginshikan jaridu da sauran kafafen yada labarai.

Ya ce mutuwar Farfesa Olukotun ya bar wani gibi da ke da wahalar cikawa, yana mai cewa za a yi kewar marigayi masanin kimiyyar siyasa, musamman saboda gudunmawar da ya bayar a fannin ilimi.

Gbajabiamila ya yi addu’ar Allah ya baiwa Farfesa Ayo Olukotun hutu na har abada, ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure rashin. Shugaban majalisar ya mika sakon ta’aziyya ga ‘yan jarida da malaman jami’o’in kan rashin.

A lokacin rayuwarsa, Farfesa Olukotun ya yi karatu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, da Jami’ar Legas da Jami’ar Jihar Legas.

Ya kasance malami mai ziyara a fannin hulda da kasa da kasa a Jami’ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife da kuma Oba Sikiru adetona Farfesan Shugabancin Gwamnati, Sashen Kimiyyar Siyasa, Jami’ar Olabisi Onabanjo, Ago-Iwoye, Jihar Ogun.

Ya kuma kasance shugaban Sashen Kimiyyar Siyasa da Dean, Faculty of Social Sciences a Jami’ar Lead City, Ibadan. A lokuta daban-daban, ya jagoranci kwamitin Edita na Daily Times kuma ya rubuta ginshiƙan mako-mako ga jaridar da kuma jaridun The Guardian, The Punch da Compass.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *