Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Buhari Ya Rattaba Hannu A kan kudirin Dokar kula Da lafiyar Kwakwalwa

Aisha Yahaya, Lagos

0 157

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudirin dokar kula da lafiyar kwakwalwa da majalisar dattawa da ta wakilai suka daidaita a shekarar 2021, ya zama doka.

 

 

Karanta kuma: Gwamnan jihar Yobe ya rattaba hannu kan kudirin dokar kula da lafiya guda biyu

 

 

Da yake tabbatar da rattaba hannun, shugaban kungiyar likitocin Asibitin mahaukata ta Najeriya, Farfesa Taiwo Obindo ya ce “Karshe na sama da shekaru 20 na kokarin da kungiyar likitocin kwakwalwa ta Najeriya ta  yi a yanzu tana da wata doka kan kula da lafiyar kwakwalwa kuma muna wani bangare na anfani da Aiyukan kula na Zamani.” 

 

 

Ya bayyana hakan a matsayin babban taimako ga harkar kula da lafiyar kwakwalwa da kuma aiki da ita a kasar.

 

 

Wasu daga cikin tanade-tanaden wannan doka da ta maye gurbin Dokar Lunacy ta 1958 masu aiki sun yi Allah wadai da rashin samar da kwararru a sashen Kula da Lafiya a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da Asusun Kiwon Lafiyar Ƙwararru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *