Hukumar kula da kayayyakin more rayuwa ta kimiyyar injiniya ta kasa, NASENI ta samu kason naira biliyan 35.6 domin gudanar da manyan ayyuka.
Mataimakin shugaban hukumar Farfesa Mohammed Haruna shi ya bayyana haka ga manema labarai na gidan gwamnatin jihar yayin da ya yi musu bayani Jim kadan da ganawar shi da shugaban kasa Muhammadu Buhari akan ayyukan NASENI.
Ya ce hukumar ta samu wannan kason ne a kashi 3 na shekarar da ta gabata, 2022.
Farfesa Haruna ya bayyana cewa rabon na cikin kashi daya na kason da gwamnati ke samu na asusun tarayya.
Ya kuma bayyana cewa hukumar ta sake samun Naira biliyan 1.2 wanda ita ma ta samu a daidai lokacin da hukumar tara haraji ta kasa ta tara nata daga masana’antun .
Tsawon kwata na uku da ake bitar, ya ce ya hada da ayyuka da kudaden hukumar daga ta gudanar daga watan Yuli zuwa Satumba 2022.
Yayin da yake bayyana yadda za a yi amfani da wannan kason, mataimakin shugaban hukumar ta NASENI ya ce ;
“Daga cikin abubuwan da za a yi amfani da wadannan kudade har da samar da kayan aikin dakin gwaje-gwaje na makarantun sakandarenmu a cikin gida. Muna kuma amfani da kudin wajen samar da jiragen sama da wasu kayan aikin da suka shafi tsaro a zaman hadin gwiwarmu da bangaren tsaro,” inji shi.
Bugu da kari, ya ce hukumar ta aiwatar da wani shiri na bincike da ci gaba, inda aka gano muhimman bangarorin ci gaban kimiyya da injiniya tare da manyan makarantun kasar nan.
A Bangaren kasa da kasa, Farfesa Haruna ya sanar da ‘yan jarida cewa NASENI na kuma kera kayan dakin gwaje-gwaje na kimiyya ga wasu kasashen Afirka kamar Kamaru, Uganda da Cote D’Ivoire da dai sauransu.
“Mun karɓi fom ɗin odar daga Uganda, Suna son samar da kayan aikin dakin gwaje-gwaje kuma wannan shine tushen kudaden shiga ga gwamnati. Kamaru da Cote D’Ivoire ma suna daukar nauyin wadannan kayayyaki kuma biyan kudin ya shiga cikin asusun hadakar kudaden shiga,” in ji shi.
Leave a Reply