Take a fresh look at your lifestyle.

Kevin McCarthy Ya Ci Zabe Shugaban Majalisar Wakilan

Aisha Yahaya, Lagos

0 231

An zabi Kevin McCarthy a matsayin Kakakin Majalisar Wakilan Amurka a cikin zazzafar musayar ra’ayi da kusan ‘yan jam’iyyar Republican suka yi ta kai ruwa rana.

 

 

Rahoton ya ce, an dauki zagaye 15 na zaben Mr. McCarthy kafin ya lashe zaben, duk da cewa jam’iyyarsa ce ke da rinjaye a zauren majalisar.

 

 

Mr. McCarthy ya samu kuri’u 216 daga cikin 428 da aka kada a yammacin jiya Juma’a.

 

 

Yayin da Hakeem Jeffries na New York Democrats bakar fata na farko da ya jagoranci jam’iyya a Majalisa ya samu kuri’u 212.

 

 

A halin da ake ciki, an gudanar da gangamin matsin lamba kai tsaye a zauren majalisar yayin da aka bukaci dan tawayen jam’iyyar Matt Gaetz ya zabe Mr. McCarthy.

 

Dan majalisar Florida na cikin masu rike da mukamai shida da suka yi murabus a yammacin ranar Juma’a.

 

 

Zafafan al’amuran Tun da farko, a cikin zazzafar fushi cikin ɗakin, Mista Gaetz ya kusan kai wa ɗan majalisa Mike Rogers mai goyon bayan Mista McCarthy duka.

 

 

 

Da yake magana bayan tabbatar da shi, Mista McCarthy ya rubuta a shafin Twitter: “Ina fatan abu daya na bayyana bayan wannan makon: Ba zan taba yin kasa a gwiwa ba, Kuma ba zan nuna gajiya da kasala ta ga da  jama’ar , Amurka ba.”

 

 

Shugaban Amurka Joe Biden ya taya Mr. McCarthy murnar nasarar da ya samu, ya kuma ce yana fatan yin hadin gwiwa da jam’iyyar Republican.

 

 

“Mutanen Amurka na tsammanin shugabanninsu sun yi mulki ta hanyar da za ta fifita bukatunsu fiye da komai, kuma abin da ya kamata mu yi ke nan a yanzu,” in ji shi.

 

 

Duk da haka, ‘yan Republican sun riga sun yi alkawarin kaddamar da bincike kan harkokin kasuwanci da gudanar da harkokin iyali na Mista Biden.

 

 

Shugaban majalisar ya tsara majalisa da kuma kula da harkokin majalisa wannan shine Mukamin  shi na biyu a kan kujerar shugabancin kasar bayan mataimakin shugaban kasar Amurka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *