Take a fresh look at your lifestyle.

Saudiyya Ta Yiwa Budurwar Ronaldo Gyaran Dokar Aure

0 158

Saudiyya na shirin gyara dokar aurenta domin baiwa sabon tauraron dan wasan Kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr da aka siyo Cristiano Ronaldo damar zama da abokiyar zamansa Georgina Rodriguez.

 

Dokar aure a Saudiyya ta haramtawa namiji da macen da ba su da aure zama tare .

 

Sai dai, kafar yada labaran Spain, ta bayyana cewa Ronaldo da Rodriguez za su zauna tare a kasar Saudiyya saboda ba za a hukunta su ba saboda karya doka.

 

Ronaldo ya koma Al Nassr ne daga Manchester United bayan da aka soke kwantiragin shi da kungiyar bayan  yarjejeniya da juna.

 

Ya ce ya zabi shiga kulob din na Saudiyya ne saboda yana son ya taimaka wajen bunkasa harkokin wasanni a yankin da kuma zama jagora da abun koyi ga matasa masu tasowa a can.

 

Fitaccen dan wasan na Portugal ya ci gaba da cewa ya zabi shiga kungiyar Larabawa ne saboda ya samu karbuwa da cin nasara a Turai.

 

Yarjejeniyar da aka kulla da Al Nassr tana biyan fam miliyan 173 a duk shekara, wanda hakan ya sa Rolando ya zama dan wasan kwallon kafa mafi tsada a duniya.

 

Al Nassr ta lashe gasar Larabawa sau tara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *