Take a fresh look at your lifestyle.

Masu Zanga-zangar Sudan Sun Koma Kan Tituna

0 141

A Sudan, daruruwan masu zanga-zangar sun fito kan titunan babban birnin kasar, Khartoum, ranar Alhamis, domin neman shugabannin sojojin kasar su sauka daga karagar mulki.

 

Masu zanga-zangar sun kuma yi watsi da yarjejeniyar da aka cimma makonnin da suka gabata na mika mulki a hankali ga shugabannin farar hula.

 

Wani juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Oktoban 2021, kwatsam ya kawo karshen yarjejeniyar mika mulki ta dimokradiyya da aka yi da shugabannin masu zanga-zangar.

 

“Wannan tattakin magana ce ta gaskiya, kuma ta gaskiya cewa mulkin al’uma ne. Sojoji na bukatar komawa bariki, sannan Janjaweed (Rapid Support Forces, Ed.) ya rusa su, kuma babu sarari ga hukumar soja a mulki ko tattalin arziki kuma dole ne a warware duk matsalolin da ya shafi kasar bisa ga kundin tsarin mulki tare da sabon akida wanda ke ba da ayyuka da iko ga sojoji don kare iyakoki da tsarin dimokuradiyya,” in ji mai fafutukar siyasa, Khaled Soliman.

 

Kungiyar Resistance Committees ce ta jagoranci zanga-zangar ta ranar Alhamis, kungiyar da ta kuma yi watsi da duk wata tattaunawa da shugabannin sojojin Sudan, Janar Abdel-Fattah Burhan da Janar Mohammed Hamdan Dagalo.

 

“Mun fito yau don dawo da kasar farar hula kuma muna kira a fili ga sojoji da su koma bariki kuma a wargaza Janjaweed (Rapid Support Forces, Ed.)”, in ji Othman al-Hady mai zanga-zangar.

 

A watan da ya gabata, shugabannin sojojin biyu sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta ”tsari” tare da babbar kungiyar masu rajin kare demokradiyya ta Sudan.

 

Yarjejeniyar da aka yi tsakanin shugabannin soji da na farar hula, ta kuma kauce wa wasu muhimman batutuwan siyasa da suka shafi adalci na rikon kwarya, da yin kwaskwarima ga aikin soja, manufar da ta yi alkawarin ganin bangarori daban-daban masu dauke da makamai a Sudan sun hade cikin rundunar yaki guda daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *