Dan takarar gwamnan jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar PDP, Alhaji Isa Ashiru ya yi kira ga wadanda har yanzu ba su karbi katin zabe na dindindin ba, PVC, da su gaggauta yin hakan.
Ashiru ya bayyana cewa canjin da suke son gani a jihar Kaduna zai yi tasiri ne kawai idan suna da katin Zabe,PVC.
Dan takarar gwamna na PDP ya yi wannan kiran ne a garin Saminaka da ke karamar hukumar Lere yayin da yake karbar wadanda suka sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress, APC da sauran jam’iyyu zuwa PDP.
Ya roki masu zabe da su ziyarci ofisoshin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, domin karbar nasu katin Zabe, inda ya bayyana cewa, ofisoshin INEC suna budewa daga karfe 9 na safe zuwa 3 na rana a kullum.
Ashiru, wanda ya shafe mako guda yana rangadin kananan hukumomin Kaduna ta Kudu da Sanata ta tsakiya, ya nemi alfarmar sarakunan wadannan gundumomin.
Ya karbi wadanda suka sauya sheka tare da tsohon gwamnan jihar, Sanata Ahmed Makarfi, shugaban jam’iyyar na jihar, Hassan Hyet, da sauran jiga-jigan jam’iyyar PDP bayan ya ziyarci daukacin sarakunan karamar hukumar Lere.
Makarfi wanda shi ma ya yi magana a lokacin da yake karbar wadanda suka sauya sheka, ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar PDP da su hada kai domin ganin an samu saukin hana gwamnatin APC a jihar cin nasara.
“Idan muna son mu cire APC, dole ne mu hada kai saboda mutanen kaduna sun kosa su fidda su daga mulkin jihar Kaduna,” inji shi.
Leave a Reply