‘Yan sandan Jamus sun tsare wani dan kasar Iran bisa zargin shi da shirya kai harin ta’addanci, kamar yadda mahukunta a kasar suka sanar a yau Lahadi.
‘Yan sanda a yammacin birnin Munster sun ce mutumin mai shekaru 32 da haihuwa ya sayo wasu abubuwan da ba a tantance adadinsu na gubar cyanide da ricin ba, a shirye-shiryen kai wa “Harin da suke yi.
An tsare wanda ake zargin ne, sakamakon wani bincike da babban ofishin da ke North Rhine-Westphalia mai kula da harkokin ta’addanci, a wani sashi na ofishin mai gabatar da kara na Düsseldorf, ya yi, a cewar ‘yan sanda.
‘Yan sanda sun kwaso kayan a yayin da ke binciken gidan wanda ake zargin a birnin Castrop-Rauxel kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.’
An tsare wani mutum dangane da lamarin, ba tare da bayar da karin bayani ba, in ji ‘yan sandan.
Leave a Reply