Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, (INEC) ta ce mutane 32,684 da suka yi rajista a jihar Legas sun karbi katin zabe na dindindin (PVCs).
Hukumar a cikin bayanan ta na yau da kullun kan karbar PVCs da ta fitar ranar Asabar a Abuja, babban birnin ta bayyana cewa 15,286 daga cikin wadanda suka yi rajistar zabe a Legas da suka karbi PVC mata ne yayin da 17,398 maza ne.
Hukumar ta kuma bayyana cewa mutane 13,703 da suka yi rajista sun karbi katin zabe su a jihar Edo.
Karanta kuma: 2023: INEC Za Ta Fara bada Katin zaben ( PVC ) a unguwanni.
INEC ta mayar da aikin ne a duk fadin kasar nan, na kabar katin zabe a matakin rajista daga ranar 6 ga watan Janairu zuwa 15 ga watan Janairu, daga nan kuma za a mayar da shi ofisoshin kananan hukumomin ta har zuwa ranar 22 ga watan Janairu.
Leave a Reply