Take a fresh look at your lifestyle.

Najeriya Za Ta Fara Canjin Noma Domin Bunkasa Tattalin Kasa -Masani

Aisha Yahaya, Lagos

0 200

Najeriya na shirin fara aikin noma cikin gaggawa domin bunkasa tattalin arzikin kasar.

 

 

Wani kwararre, tsohon babban jami’in kididdiga kuma shugaban hukumar kididdiga ta kasa (NBS), Dokta Yemi Kale ya bayyana haka, bayan wani bincike da aka gudanar a fadin kasar nan ya nuna cewa,  mafiya talauci a kasar nan suna noma ne kawai.

 

 

Ya kuma yi kira da a inganta harkar noma a babban mataki, ya kara da cewa, saboda kalubale da dama nada alaka da noma kamar yadda ake fama da matsalar sauyin yanayi, aiki tukuru, da rashin horo mai tsanani kan muhimman abubuwa, hakan ba za a dogara da shi ba wajen samun abinci. 

 

 

“Noma na taka muhimmiyar rawa wajen kawo sauyi ga tattalin arzikin kasar. Don haka, don haɓaka tattalin arziƙi, dole ne a sami sauye-sauyen aikin gona cikin gaggawa.

 

 

 “Wannan za a iya cimma shi ne kawai  idan Najeriya ta samu ci gaba, galibi bangaren noma ne mai dorewa da kuma tsarin noman kasuwanci ta hanyar amfani da fasaha,” in ji shi. 

 

 

A halin da ake ciki, Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) ta ce sama da kashi 70% na ‘yan Najeriya na yin noma musamman domin rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *