Take a fresh look at your lifestyle.

Archbishop ya ba da Shawarar Gaggauta Karbar katunan Zaɓe na Dindindin

2 158

Archbishop Emeritus kuma Dean, Cocin Anglican Communion Najeriya, Maxwell Anikwenwa, ya shawarci masu kada kuri’a da su karbi katin zabe na dindindin (PVCs) don ba su damar yin amfani da ikonsu a babban zabe mai zuwa.

 

 

Archbishop Anikwenwa ya yi wannan kira ne a lokacin bikin sadaukar da cocin Our Saviour’s da ke Awka a jihar Anambara a kudancin Najeriya ,da Archbishop na lardin Nijar Most Rev. Alexander Ibezim ya yi.

 

 

Ya ce ya kamata ‘yan Najeriya suci gaba da kada kuri’u cikin hikima a lokacin zabe ba tare da la’akari da addini ba, ya kuma bayyana wadanda ke korafin sakamakon zabe a lokacin da suka ki kada kuri’a.

 

 

“Kowane dan Najeriya, ba tare da la’akari da akidar addini ba, ya kamata ya yi rajista ya karbi nasa PVC domin su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na kada kuri’a a lokacin zabe.

 

 

“Yana da matukar muhimmanci ga kowane dan Najeriya ya kada kuri’a a lokacin zabe.

 

 

Duk wanda bai bayar da gudunmawa a cikin wannan tafiyar ba, na sauke muhimmin aiki ,bai kamata ya yi korafi ba.

 

 

 “Amma idan ba ku yi zabe ba, ba ku bukatar yin korafi”. in ji Archbishop Anikwenwa.

 

Tun da farko a cikin wa’azinsa mai taken “Kada ku daina”, wanda aka ɗauko daga littafin Matta sashe na 15:21, Archbishop Ibezim ya bukaci jama’a da kada su bar ƙalubalen rayuwa ya hana su yin ibada da yi wa Allah hidima.

 

 

Ya kuma yabawa limaman cocin bisa irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban cocin da kuma fadada shi, inda ya bukace su da kada su yi kasa a gwiwa, musamman wajen gudanar da ayyukan da ake so.

 

 

“Bauta wa Allah yana kawo mu’ujizai. Kada ka ƙyale ƙalubalen rayuwa su hana ka bauta wa Allah; kuma kada ku yi gunaguni a duk lokacin da aka ce ku yi wani abu a cikin coci domin gata ce ku yi wa Allah aiki,” a cewar shi.

 

 

A nasa bangaren, shugaban kwamitin sadaukarwar, Cif Chukwuemeka Orjiakor, ya yi godiya ga Allah da ya kasance cikin wannan taro na zamani, inda ya bukaci jama’a su hada karfi da karfe don ganin an kammala shirin a kan lokaci.

 

 

Daya daga cikin jiga-jigai a wajen bikin Samuel Nwofor, yayi godiya ga Allah saboda saurin ci gaban ruhi da lambobi da cocin ya samu tun kafuwar shi.

Nwofor, dan takarar jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), Awka ta Kudu 1, a majalisar dokokin jihar Anambara, ya kuma bayyana farin cikin shi da yadda masu kada kuri’a suka samu kyakykyawan fitowa a rumfunan karbar katin zabe na PVC.

 

 

Ya kuma bukaci wadanda har yanzu ba su karbi nasu ba da kada su zauna a gida su yi korafin masu rike da madafun iko, inda ya ce babu shakka Za’a kirga kuri’unsu , kuma yin hakan shine daidai.

2 responses to “Archbishop ya ba da Shawarar Gaggauta Karbar katunan Zaɓe na Dindindin”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *