Take a fresh look at your lifestyle.

Gabon Ta Samu Mataimakiyar Shugaban Kasa Mace Ta Farko

0 168

Shugaban kasar Gabon, Ali Bongo ya nada Firai ministar kasar mace ta farko Rose Raponda a matsayin mataimakiyar shugaban kasa tare da nada sabon Firaministan da zai maye gurbinta.

 

Ms. Raponda kuma ita ce mace ta farko da aka nada mataimakiyar shugaban kasa a Gabon.

 

Rahoton ya ce dole ne ta shiga wani yanayi mai ban sha’awa a matsayin Firayim Minista bayan yunkurin juyin mulki a 2019 yayin da Bongo ke jinya na tsawon lokaci sakamakon bugun jini.

 

 

Yayin da, tsohon minista, Alain Nze zai maye gurbin Ms. Raponda kuma ya kafa sabuwar gwamnati, babban sakataren Bongo, Jean Teale ya ce a cikin wata sanarwa ta bidiyo da aka wallafa a shafin Twitter na fadar shugaban kasa.

 

An nada Ms. Raponda Firayi Minista ne a watan Yulin 2020 bayan da magabacinta ya yi murabus, duk da cewa ta kasance ministar tsaro kafin nan.

 

An kuma nada ta a matsayin ministar kasafin kudi a shekarar 2012 kafin a zabe ta a matsayin magajin garin Libreville babban birnin kasar a shekarar 2014, inda ta zama mace ta farko da ta rike wannan mukamin tun shekara ta 1956.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *