Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan murnar cika shekaru 64 da haihuwa, wanda ya yi daidai da 12 ga watan Janairu, 2023, inda ya bayyana farin cikin shi ga majalisar dokokin kasar.
Shugaba Buhari ya bi sahun ‘yan uwa da abokan arziki da ‘yan siyasa wajen taya shugaban majalisar dattawan kasar murna, wanda ya yi fice a matsayin daya daga cikin gogaggun ‘yan majalisar dokoki a kasar nan, inda ya shafe shekaru takwas a majalisar wakilai, 1999-2007, kuma ya kai kusan shekaru 12 a majalisar dattawa.
Shugaban ya tabbatar da cewa Sanata Lawan bayan ya bar aikinsa na malami kuma mai bincike, ya yi amfani da dimbin iliminsa wajen tsara manufofi da karfafa dimokuradiyya a Najeriya ta hanyar bayar da shawarar samun nasara ga dukkan masu ruwa da tsaki.
Shugaban ya lura da tsoma bakin da shugaban majalisar dattawa ya yi a tarihi, musamman samar da shugabanci na lumana da ga majalisar dokokin kasar ta 9 wanda ya haifar da nasarori da dama ga kasar nan kan doka da zartar da kudirorin doka.
Shugaba Buhari ya yi addu’ar Allah ya kara wa Sen. Lawan da iyalansa lafiya.
Leave a Reply