Tsohon dan wasan Super Eagles, Ogenyi Onazi ya koma kungiyar Premier ta Bahrain, Gabashin Riffa.
Onazi ya koma kungiyar Bahrainain daga kulob din Seria D na Italiya, Casertana FC inda ya buga wasan karshe.
Dan wasan mai shekaru 30, ya samu horo da kungiyar kwararrun kwallon kafa ta Najeriya, Remo Stars a watan da ya gabata.
Onazi ya yi balaguro da fice a kungiyoyi a Italiya da Turkiyya da Lithuania da Saudi Arabiya da kuma Denmark.
Onazi dai ya kasance memba a tawagar Super Eagles da ta lashe gasar cin kofin Nahiyar Afirka na shekarar 2013 a Afrika ta Kudu.
Leave a Reply