Take a fresh look at your lifestyle.

Ranar Majalisar Dillalan Jiragen Ruwa ta Najeriya za ta Gudana a Legas

0 204

Kungiyar Hadin Kan Sufurin Jiragen Ruwa ta Afrika (UASC) da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NSC), sun shirya gudanar da bikin kwanaki uku na ranar jigilar kayayyaki tsakanin 16 zuwa 18 ga watan Janairu.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne zai kaddamar da taron wanda Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya ke ba da iko.

Taken taron shi ne “Yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci ta Afirka (AfCFTA): ingantaccen dandali ga masu jigilar kayayyaki na Afirka don shiga cikin kasuwancin duniya.” 

A yayin taron, ana sa ran mambobin kungiyar ta UASC za su sake duba tsarin AfCFTA tare da samar da taswirar yadda za a magance kalubalen.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *