Kwamandan rundunar, MNJTF, Maj.-Gen. Abdul-Khalifah Ibrahim, ya yi kira da a ci gaba da kokarin kawo karshen ayyukan kungiyoyin ta’addanci a yankin tafkin Chadi.
A wata sanarwa Kakakin MNJTF Lt.-Col. Kamarudeen Adegoke, da ya fitar a ranar Asabar, ya ce Ibrahim ya yi wannan kiran ne a yayin bikin kaddamar da ayyuka na shekarar 2023 a birnin N’Djamena na kasar Chadi.
Ya kuma yabawa sojoji da ma’aikatan da suka yi aiki tare domin kawo karshen ayyukan ‘yan ta’addan Boko Haram da kungiyar ISWAP a yankin yammacin Afirka.
A cewar shi, nasarorin da aka samu a shekarar 2022 sun samu ne sakamakon hadin gwiwa a dukkan matakai, sakamakon bukatar hadin gwiwa da yaki da rashin tsaro a yankin.
Kwamandan rundunar ya bayyana fatansa na cewa, hadin gwiwa tsakanin sojoji da abokan huldar dabarun yaki zai yi galaba a kan barazanar ta’addanci da tada kayar baya a yankin a bana.
Ya kuma yabawa Jamhuriyar Chadi bisa samar da yanayi mai kyau da tsaro ga MNJTF domin gudanar da ayyukanta.
Ibrahim ya jinjina wa takwarorinsa da suka rasu wadanda suka biya farashi mai tsoka a kokarin samar da zaman lafiya a yankin tare da yin addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasashen yankin tafkin Chadi.
Ya ce taron wani yunkuri ne na kara karfafa nasarorin da kungiyar MNJTF ta samu wajen yaki da ta’addanci.
Tun da farko, mataimakin kwamandan rundunar, Brig.-Gen. Assoualai Blama ya godewa kwamandan rundunar bisa salon jagorancin shi, wanda ya ce ya nuna a cikin dimbin nasarorin da MNJTF ta samu a cikin shekarar da ta gabata.
Blama ya kuma tabbatar wa kwamandan cewa sojoji da ma’aikata da sauran sassan a shirye suke don cika aikin MNJTF na tabbatar da dawo da zaman lafiya da tsaro a yankin baki daya.
A cewar shi, kungiyar ta MNJTF ta samo asali ne daga kwakkwaran kudurin shugabannin kasashe da gwamnatocin kasashen yankin tafkin Chadi da ke fuskantar barazanar ta’addancin Boko Haram.
“Sun yanke shawarar bayar da amsa bai-daya ta hanyar aiwatar da rundunar hadin gwiwa ta musamman – MNJTF.
“A matsayin tawaga, MNJTF za ta ci gaba da yin aiki tukuru wajen magance ayyukan Boko Haram da ISWAP har sai an kawo karshen yaki da ta’addanci,” in ji shi.
Blama ya kuma godewa abokan hulda daban-daban bisa gagarumin goyon bayan da suke bai wa kungiyar ta MNJTF tare da yin kira da a kara kaimi.
Ya zayyana wasu nasarorin da rundunar ta samu da suka hada da ayyukan da rundunar ta samu nasara kamar su Operation Lake Sanity da mayar da dubban ‘yan gudun hijira zuwa gidajen kakanninsu, ya kuma yi alkawarin kara yin wani abu a wannan sabuwar shekara.
Leave a Reply