Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce an shawo kan gobarar da ta kama hedikwatar ta da ke Bampai ba tare da samun asarar rai ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Haruna Kiyawa a wata sanarwa ,ya ce jami’an hukumar kashe gobara ta jihar ne suka shawo kan gobarar.
“Ba a yi asarar rai ba kuma ba a sami rahoton wani rauni ba. Jami’an kashe gobara sun shawo kan gobarar,” inji shi
A cewar shi, gobarar ta cinye shingen gudanarwa da ke hawa na farko na hedikwatar ‘yan sandan jihar Kano, Bompai.
“Ofisoshin da gobarar ta kone a rukunin gidajen sun hada da:; Ofishin Shugaban Shelkwatar, DC Ofis din hada hadar kudi da Gudanarwa, AC Ofishin gudanar da aiyyuka, AC Ofishin harkokin yau da kullum daOfishin Jami’in hulda da Jama’a da sauransu,” in ji shi.
Ya ce bayanan hukumar da kuma ofishin kwamishinan ‘yan sanda ba su da tushe domin an shawo kan gobarar kafin ta taba wuraren.
Ya ce, Mai girma Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, DR. Nasiru Yusuf Gawuna ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, inda ya jajanta ma rundunar NPF, IGP, AIG Zone 1 kuma a madadin gwamnatin jihar Kano ya yi alkawarin taimaka wajen sake gina wannan katafaren ginin da ya kone.
“Kwamishanan ‘yan sandan jihar CP Mamman Dauda, psc(+) da jami’ai da jami’an rundunar ‘yan sandan Kano ne suka tarbi mataimakin gwamnan a wurin,” in ji shi.
Leave a Reply