Take a fresh look at your lifestyle.

NCDC ta tabbatar da samun sabbin mutane 29 masu dauke da cutar COVID-19 a Najeriya

0 76

Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta tabbatar da samun karin mutane 29 da suka kamu da cutar COVID-19 a jihohi shida na Najeriya.

 

 

An gano wannan adadin ne tsakanin 7 ga Janairu zuwa 13 ga Janairu, 2023. Jihohin da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 su ne: Legas (15); FCT (5); Kano (4); Nasarawa (3); Kaduna (1) da Plateau (1).

 

 

A cikin wata sanarwa da NCDC ta fitar a ranar Lahadin da ta gabata ta ce: “Daga ranar 7 zuwa 13 ga Janairu, 2023, an samu sabbin mutane 29 da aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya… Cibiyar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (EOC), wacce ke aiki a mataki na 2, tana ci gaba da daidaita ayyukan mayar da martani na kasa. “. Hukumar NCDC ta ce.

 

 

Bisa kididdigar da aka samu, ya zuwa yanzu, an tabbatar da masu dauke da cutar guda 266,492, an kuma sallami mutane 259,858, sannan an samu rahoton mutuwar mutane 3,155 a jihohi 36 da babban birnin tarayya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.