Asusun Ba da Lamuni na Duniya IMF,ya ce, hasashen tattalin arzikin duniya zai iya raguwa da kashi 7%, idan tattalin arzikin duniya ya yay i sanadiyar rarrabuwar kawuna ,bayan shekaru da dama .
A wani sabon rahoton ma’aikata IMF tace asarar na iya kaiwa kashi 8-12% a wasu kasashe, idan har aka lalata fasaha.
Asusun na IMF ya ce ko da takaitaccen rarrabuwar kawuna na iya aske kashi 0.2% na GDP na duniya, amma ta ce ana bukatar karin aiki don tantance kudaden da ake kashewa ga tsarin hada-hadar kudi na kasa da kasa da kuma cibiyar kare kudi ta duniya (GFSN).
Sanarwar da aka fitar a yammacin Lahadin da ta gabata, ta yi nuni da cewa, hauhawar kayayyaki da jari a duniya ya yi kamari bayan rikicin kudi na duniya na 2008-2009, da karuwar takunkumin cinikayya da aka samu a shekarun baya.
Rahoton ma’aikatan ya ce “Cutar COVID-19 da kuma mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine sun kara gwada dangantakar kasa da kasa da kuma kara nuna shakku game da fa’idar dunkulewar duniya.”
Leave a Reply