Take a fresh look at your lifestyle.

Babu Masauki Ga Baƙi’- Magajin Garin New York

Aisha Yahaya, Lagos.

0 249

Magajin garin New York, Eric Adams, ya yi tattaki zuwa birnin El Paso da ke kan iyakar Mexico a ranar Lahadin da ta gabata kuma ya ba da sanarwar cewa “babu daki a New York don jigilar bas din bakin haure zuwa birni mafi yawan jama’a a Amurka.” 

 

 

 

Dan jam’iyyar Democrat Eric Adams, shi ma ya soki gwamnatin shugaban Amurka na Democrat Joe Biden, yana mai cewa, “yanzu ne lokacin da gwamnatin kasa za ta yi aikinta” game da rikicin bakin haure a kan iyakar kudancin Amurka.

 

 

 

KARANTA KUMA: Biden ya ziyarci iyakar Amurka-Mexico

 

 

 

Ziyarar da wani magajin garin na New York ya kai wani birnin kan iyaka da ke kudancin kasar game da bakin haure da ba a taba yin irinsa ba.

 

 

 

Jihohin da ke karkashin jam’iyyar Republican sun yi jigilar bas-bas na bakin haure a arewa zuwa New York da wasu garuruwa. Hakan ya ta’azzara matsalar gidaje a New York da kuma matsalar rashin matsuguni a birnin.

 

 

 

Tafiyar Adams zuwa El Paso zuwa ne bayan da ya ce kwararar bakin hauren zuwa New York na iya jawo asarar dala biliyan 2 a birnin yayin da tuni garin ke fuskantar gibin kasafin kudi.

 

 

 

A cikin ‘yan watannin nan, gwamnonin ‘yan Republican na Florida da Texas sun aike da dubban bakin haure da ke neman mafaka a Amurka zuwa garuruwan da ‘yan siyasar jam’iyyar Democrat ke gudanarwa, ciki har da New York, Chicago, da Washington, D.C.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *