Take a fresh look at your lifestyle.

Aisha Yahaya, Lagos

0 296

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta yi nasarar kashe wani dan bindiga, tare da cafke wasu mutane biyu da ake zargi, sannan ta kuma kwato wata karamar bindiga kirar AK47 mai dauke da harsashi guda hudu.

 

 

 

Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, PPRO, DSP Muhammad Jalinge, da aka rabawa manema labarai a Kaduna.

 

 

 

Ya kara da cewa, “a ci gaba da farmakin da rundunar ‘yan sandan ta kai a kan ‘yan ta’adda, ‘yan bindigar da ke yankin Rigachikun sun samu kiran da ‘yan bindigar suka kai hari a wani kauye, kuma jami’an suka yi gaggawar tattarewa tare da dakile yunkurin ‘yan bindigar na yin garkuwa da mazauna garin. 

 

 

 

“Jami’an tsaro sun samu labarin cewa ‘yan bindiga sun kai farmaki gidan wani Umar Ibrahim da ke kauyen Amana Maimadachi, bayan samun rahoton halin da ake ciki, jami’an tsaro tare da sauran masu ruwa da tsaki a harkar tsaro sun yi gaggawar tafiya inda suka kama ‘yan bindigar tare da dakile su na yunkurin sace ‘yan kasa.”

 

 

 

A wata sanarwar, a farmakin da aka kai cikin dabara, an kashe daya daga cikin ‘yan bindigan sanye da kakin soja, yayin da wasu suka tsere da munanan raunukan harbin bindiga, yayin da aka samu nasarar kwato bindiga kirar AK47 dauke da harsashi guda hudu daga hannun ‘yan fashin.

 

 

 

Jalinge ya kara da cewa, a wani labarin makamancin haka, jami’an rundunar ‘yan sandan da ke aiki da sashen Saminaka sun yi aiki da sahihan bayanai inda suka kai wani samame cikin nasara a yankin Warsa Piti da ke Saminaka, a karamar hukumar Lere, inda suka kama wasu ‘yan bindiga biyu.

 

 

 

Ya ce a lokacin da aka gudanar da kwakkwaran bincike a kansu, an kwato bindiga kirar GPMG na cikin gida tare da harsashi guda shida da kuma bindigar dawa.

 

 

 

“Bayan bincike na farko, wadanda ake zargin sun amsa laifin mallakar makaman kuma a halin yanzu suna taimakawa ‘yan sanda wajen bincike inda daga karshe za a gurfanar da su gaban kotu.” 

 

 

 

Ya bayyana cewa kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kaduna, CP Yekini Ayoku psc(+), mni, yayin da yake yaba da jajircewar da jami’an suka yi wajen gudanar da wadannan ayyuka da sauran ayyuka a fadin jihar, ya bayar da umarnin gudanar da sintiri a yankin baki daya domin kamo ‘yan sandan guduwa ‘yan fashin da suka samu raunuka da kuma yin cikakken bincike kan wadanda aka kama tare da binciki laifukan da suka aikata.

 

 

 

Ya kuma tabbatar wa da al’umma na kwarya-kwaryar kuduri na yin duk abin da ya dace don ci gaba da inganta harkokin tsaron jama’a tare da yin kira ga kowa da kowa da su baiwa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro goyon baya da hadin kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *