Take a fresh look at your lifestyle.

APC Ta Kaddamar Da Gidauniyar Gina Sakatariyar Jam’iyyar A Katsina

Kamilu Lawal,Katsina.

6 233

Jam’iyyar APC reshen jihar Katsina ta gudanar da taron domain karbar gudummuwar gina sakatariya mallakin ta a jihar

 

Bikin neman gudummuwar a tsakanin yayan jam’iyyar wanda ya gudana a harabar gina sabuwar sakatariyar ya samu halartar wakillan uwar jam’iyyar na kasa da shugabab taron  ministan harkokin sufurin jiragen sama sanata Hadi Sirika da jami’an gwamnati da yan kasuwa da sauran mask ruwa da tsaki  kalkashinn jagorancin gwamnan jihar Aminu Bello Masari

 

Da yake jawabi a wajen taron gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa kammala ginin sakatariyar jam’iyyar zai taimaka wajen gudanar da aiyuka jam’iyyar da mambobin ta cikin sauki da walwala

 

Gwamna Masari wanda ya bayyana cewa ana sa ran kammala ginin sakatariyar kafin rantsar da sabuwar gwamnati mai zuwa ya kuma bayyana ginin sakatariyar a matsayin wani mahimmin cigaba da zai tabbatar da bunkasa da daukakar jam’iyyar

 

Ya godema shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa bayar da gudummuwar sa wajen cigaban gina sakatariyar a jihar ta Katsina

 

Kamar yadda ya bayyana ta hanyar sa ne aka samu gudummuwa daga yayan jam’iyyar da kamfanoni da suka aiko da gudummuwar su daga fadin najeriya

 

Gwamna Masari ya kuma godema magoya bayan jam’iyyar da suka bada gudummuwar su tare da kira ga sauran yayan jam’iyyar da su bada tasu gudummuwar domin a kamnala aikin cikin lokaci

 

Tun farko, a nasa jawabin shugaban taron Sanata Hadi Sirika ya ya yabama gwamnan jihar da sauran wadanda suka assasa ginin sakatariyar tare ga ganin an kammala cikin kankanen lokacin da aka kayyade a watanni masu zuwa

 

Yana mai cewa karrrama  jam’iyyar ta hanyar samar mata matsugunnin na kanta abu ne mai mahimmanci saboda duk wanda kaga an zaba kalkashin jam’iyya aka zabe shi kuma dalilin mutunci jam’iyyar aka zabe shi

 

A lokacin taron an bayyana gudummuwar da aka samu daga yayan jam’iyyar da kamfanoni da jami’ai da yan kasuwa daban daban hadi da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ta APC a jihar Katsina

6 responses to “APC Ta Kaddamar Da Gidauniyar Gina Sakatariyar Jam’iyyar A Katsina”

  1. I used to be suggested this website by my cousin. I’m
    not certain whether this publish is written via him as nobody else
    know such precise approximately my trouble. You’re incredible!
    Thank you!

  2. Howdy just wanted to give you a quick heads up and let you
    know a few of the pictures aren’t loading properly. I’m not sure why
    but I think its a linking issue. I’ve tried it in two different web browsers and both show the same outcome.

  3. I’ve been browsing online more than 2 hours today, yet I never found any interesting article like yours.
    It is pretty worth enough for me. Personally, if all website owners and bloggers made good content as you did, the web will be a lot more useful
    than ever before.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *